16 Mayu 2021 - 18:12
An Bijire Wa Dokar Hana Goyan Bayan Falasdinu A Faransa

A Faransa, dubban mutane ne suka fito zanga zangar goyan bayan al’ummar Falasdinu, duk da haramcin da hukumomi sukayi na kada a fito zanga zangar.

ABNA24 : Bayanai sun ce jama’a sun fito a Paris, inda hukumomin suka haramta yin zanga zangar, inda akayi ta dauki ba dadi tsakanin masu zanga zangar da ‘yan sanda a wasu sassan birnin birnin.

A wasu sassan kuma an gudanar da zanga zangar ba tare da wata hatsaniya ba.

A wani labarin kuma an gudanar da zanga zangar ta goyan bayan al’ummar Falasdinu a birnin London na Biritaniya, inda masu zanga zangar suka nufi ofishin jakadancin Isra’ila dauke da tutocin Falasdinu.

342/